Wasu 'yan mata biyu sunyiwa dan acaba sanen kudin aikinsa gaba daya - a Zariya


Daga Muhammad Inuwa Zaria

Wani Dan acaba ya zargi wasu ‘yan mata biyu da kwashe Masa duka cinikin daya kwashe wuni guda Yana tarawa, Dan acaban dai ya zargi ‘yan matan ne bayan daya dibosu su biyu a tare.

Shidai wannan Dan acaba ya koka ne a lokacin daya duba kudinsa yaga babu komai a inda yake tarasu a cikin jikinsa, sai dai ya gaya mana yadai ji ‘yan matan biyu suna ta matsan sa alokacin da yake jaye dasu, suna ta ce Masa ya Kara gudu.

Bayan ya ajiyesu ne ya nimi kudinsa ya rasa, Hakan yasa yake shawartan ‘yan uwansa ‘yan acaba da su dunga kula sosai da aljihun su musanman na tara kudi alokacin da suka dauki passinger.

Wannan lamari ya farune daga kasuwan Zaria zuwa kofar gayan zariya.


Post a Comment

0 Comments