Daga Malam Abu Ruqayyah Zaria
Innalillahi wainna ilaihi raji'un.😭
Wannan lamari na kisan bayin Allah da'aka jefa musu bom lokacin maulidi tsakanin jiya da yau,hakika abin tashin hankali ne, abinda yafi daure mini kai shine wasu na zargin jami'an tsaro ne suka sakar musu bom,abin mamaki sukuma jami'an tsaro sunce basuda wani abu balle masaniya akan harin wannan abun akwai rainin hankali a cikin sa.
Babu yanda za'ayi ace jirgi yasaki bom akasa gane suwaye sukayi wannan aika aikan, al'amari yazama kamar wasan drama,wasan kwaikwayo,irin wainnan abubuwan Arewa kadai akema wannan cin kashin, kwankin baya mawaki aka kashe amman yan kudu sukace basu yarda ba,wanda takaima majalisa Saida tayi (silent)na wasu mintuna kafin cigaba da zaman ta,muna jiran muga wani mataki gomnatin Nigeria zata dauka wajen wainnan mutane ko sojoji ne koma basuba matakin Hukunci garesu.
Yaa ubangiji kakawo mana dauki,ka gafarta ma wainnan yan uwa namu dasuka rasa rayuwar su,ka baiwa iyalen su hakurin rashin su yaa Allah.
GGaskiya dayadGaskiya daya
0 Comments