An shiga jimami bayan rasuwar kwararriyar ma’aikaciyar gidan talabijin na NTA, Aisha Bello.
Mutuwar marigayiyar ya girgiza intanet inda ‘yan Najeriya su ka nuna kaduwarsu kan wannan babban rashi.
Yaushe marigayiyar ta rasu?
An samu rahoton rasuwar marigayiyar a jiya Lahadi 10 ga watan Disamba sai dai ba a bayyana silar mutuwar tata ba.
Legit ta tattaro cewa za a yi sallar jana’izar marigayiyar yau Litinin 11 ga watan Disamba a babban masallacin Abuja da misalin karfe 1 na rana.
Kafin rasuwarta, Aisha ta rike mukamin babbar manaja a bangaren shirin Majalisa a NTA wacce ta shafe shekaru 30 a matsayin mai labaru tun shekarun 1990.
Ta kuma yi aiki tare da kwararren ma’aikacin NTA, Cyril Stober wanda ya yi ritaya a shekarar 2019. Marigayiyar ta yi rataya a matsayin babbar manajar sashin shirin Majalisa a NTA a watan Mayun 2022.
Wane martani iyalan marigayiyar su ka yi? Iyalan marigayiyar sun fitar da sanarwa kan rasuwar inda su ka bayyana ta a matsayin mace mai kirki.
Sanarwar ta ce: "Innalillahi wa inna ilahir rajiun, Allah ya gafarta wa mamarmu Hajiya Aisha Bello Mustapha.
0 Comments