Haka Dama Najeriya Take: Wani yaro ya firgita Jim kadan bayan isowarsa Nigeria 🇳🇬


Wani karamin yaro ya kasa gaskata idanuwansa yayin da ya ga tulin mutane da yawa a filin jirgin saman Najeriya bayan ya isa kasar a ziyararsa ta farko.

Mahaifiyarsa ta bayyana cewa ziyararsa ta farko Najeriya kenan, inda ya kwashe da dariya har ya rude da ganin jama'a a filin jirgin. Ta nadi abin da ya faru mai ban dariya yayin da suke tattaunawa.

Cikin rudani a fuskarsa yaron ya kada baki yace, dama haka Najeriya take.

Matar dai ta bayyana mamakin yadda yaron ya ji, kana ta tsaya tunanin ya dan nata ke son ganin Najeriya idan ba haka ba.

Bidiyon da aka yada a kafar TikTok ta hannun @stoner_012 ya jawo cece-kuce da yawa, ya kuma sa mutane suna ta magana. 

Wasu kuwa, sun bayyana kadan daga abubuwan da zai ci karo dasu a matsayinsa na mai ziyara a kasa irin Najeriya.

Kalli bidiyon:
Daniel: "Abin babu kyau dan yaro, kada ka damu za a fada ma Tinubu ya amince da ba da kyautar Kirsimeti." 

ANUOLUWAPO OLUTOLA: 

"Ku fada masa haka siddan ake dauke wuta ana kawowa. Kada ya fara kuka."

yes_I'm_naveen: 

"Watakila ya yi zaton mutane na rayuwa a cikin daji da bishiyoyi ne a Najeriya."

MBen: 

"Shin babu mutane ne a jirgin da ya hau ya zo? Me yasa mutane za su bashi tsoro?"

Cynthia: 

"A filin jirgnin sanda kake kuma har ka fara korafi ka bari ka shigo titi mana."
@stoner_012 Ómo the boy confuse 😭😂😂 Nigeria my country 🥰♥️#tiktok #cruise #fypシ゚viral #viralNigeria ♬ original sound - STONER 🌹

Post a Comment

0 Comments