Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi tir da abin da ya faru a garin Tudun Biri da sojoji su ka kashe Bayin Allah kusan 100.
A wani jawabi da ya fitar a Facebook, Dr. Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya kira lamarin da abin takaici da ke faruwa a yankin Arewa.
Shehin yake cewa ana maida jihohin Arewacin Najeriya tamkar zirin Gaza inda sojojin Israila su ke hallaka mutanen kasar Falasdin.
Malamin addinin ya zargi hukumomi da mugun nufi da kuma yin kisan kare dangi da ganganci ga al’ummar da ke kauyukan Arewa. "Ba za ta yiwu ayi kuskure wajen harba bam ga masu fararen kaya ba.
Ana amfani da bam ne a kan sa’o’in dakarun abokan fada. Ba za a yarda da wannan ba, abin Allah-wadai ne kuma akwai wata kullaliya." -
Sheikh Ahmad Abubakar Mahmud Masanin ilmin fikihun yake cewa makiyaya su na kukan ana kashe su babu gaira babu dalili, ana harba bama-bamai a rugagensu.
Gumi ya kara maganarsa da cewa ana fuskantar matsala a yadda ake fama da rashin sanin ya kamata, yana nuni ga sojoji da hukuma.
Dr. Rijiyar Lemu ya yi tir da kisan Kaduna
A ranar Talata kuma Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu ya yi magana a kan abin da ya faru, ya kuma jajantawa al’umma.
Bayan haka, Farfesan ya bada wasu shawarwari ga mahukunta tun daga fara bincike tare da biyan diyyar duk wadanda aka rasa a harin.
Kisan Jama’a a Kaduna: Ta’aziyya Da Jan hankali Ga Mahukunta:
1. Muna mika ta’aziyyar mu da duk yan’uwa da abokan arzuki da ilahirin Musulmin Nijerya bisa ga abin bakin cikin da ya faru ranar Lahadi da ta gabata, na harin da ake zargin jirgin yakin sojojin Nijeriya ya kai wa wasu Musulmi a Kaduna, wanda ya jayo asarar rayuwa masu yawa, baya ga wadanda aka ji wa raunuka.
Muna addu’a Allah ya gafarta musu, ya sanya Aljanna ce makomarsu.
2. Sannan muna kira ga mahukunta cewa, lalle su gudanar da bincike a kan dalilan faruwar irin wannan aika-aika da wadanda suke da hannu a ciki, da daukan kwakkwaran mataki da zai dakatar da ci gaba da faruwar hakan a nan gaba.
3. Sannan lalle wajibi Gwamnati ta biya diyyar wadanda suka rasa rayukwansu da kuma wadanda aka ji wa raunuka.
4. Allah ya kawo mana zaman lafiya mai dorewa a kasarmu da sauran kasashen Musulmi baki daya.
Amin. - Sheikh Muhammad Sani Umar Rijiyar Lemu.
0 Comments