Biki: Wata matar aure ta watsawa mijinta ruwan zafi saboda ya hanata zuwa gidan biki..


Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta kama wata mata da zargin watsa wa mijinta ruwan zafi a jihar.

Wacce ake zargin, Dorcas Oluwabukola ta watsa wa mijin nata ruwan zafin ne a ranar 18 ga watan Disamba a jihar, cewar TheCable.

Mene ake zargin matar da aikatawa?

Kakakin rundunar ‘yan sanda a jihar, Benjamin Hundeyin ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Litinin 25 ga watan Disamba.

Hundeyin ya ce matar da ake zargi ta tafasa ruwan zafi tare da watsa wa mijin nata don ya ki daukarta zuwa bikin abokinshi. 

Ya ce an kama matar ce bayan an samu rahoton daga ofishin ‘yan sanda na Meiran da ke birnin a ranar da abin ya faru, cewar Radio Nigeria. 

Mene dalilin matar na watsa wa mijin ruwan zafi? 

Ma’auratan sun shirya zuwa auren ne a tare kafin daga bisani mijin ya fasa zuwa da matar inda ya yanke shawarar zuwa shi kadai. 

Wannan matakin da ya dauka shi ya jawo matsala a tsakaninsu inda har matar ta tafasa ruwan zafi tare da watsa masa a jiki.

Benjamin ya ce tuni rundunar ta fara bincike don gano bakin zaren inda ya ce a yanzu haka mijin na karbar kulawa a asibiti.

Post a Comment

0 Comments