Murna ya barke yayin da aka bayyana ranar da za'a daina shigo da mai, NNPC ya yi albishir kan ranar da matatar Kaduna zai fara aiki


Kamfanin mai na NNPC ya bayyana cewa zai dakatar da shigo da mai zuwa Najeriya a watan Disamban 2024. 

NNPC ya bayyana haka ne a jiya Juma'a 24 ga watan Nuwamba inda ya ce matatun man Najeriya za su fara aiki kafin wannan lokaci.

Yaushe matatun mai za su fara aiki?

Shugaban NNPC, Mele Kyari shi ya bayyana yayin ganawa da masu ruwa da tsaki a harkokin man fetur a kasar, cewar Arise.

Har ila yau, Kakakin Majlisar Wakilai, Honarabul Abbas Tajudden ya samu halartar taron inda ya bukaci a saka matatun a kasuwa.

Legit ta tattaro cewa dillalan man fetur sun tabbatar da fara aiki na matatar Port Harcourt inda su ka ce za ta fara aiki a watan Janairun 2024. 

Yaushe NNPC zai dakatar da shigo da mai? 

Dillalan su ka ce fara aikin matatar ta Port Harcourt zai rage farashin albarkatun mai a kasar. 
Kamfanin ya yi hasashen samun ribar naira tiriliyan 4.5 zuwa karshen wannan shekara ta 2023.

Ya ce: "Ina mai tabbatar muku da cewa zuwa karshen Disamban wannan shekara za mu fara aiki da matatar Port harcourt sai kuma matatar Warri a watan Janairu.

"Zuwa karshen 2024 matatar Kaduna za ta fara aiki yayin da za mu dakatar da shigo da mai zuwa Najeriya a karshen shekarar 2024."

Post a Comment

0 Comments