'Yan sanda sunyi nasarar cafke wasu mutum 6 da sukayi yunkurin sace taragon jirgin ƙasa a Borno


Jihar Borno – Rundunar ‘yan sanda a jihar Borno ta dakile shirin sace taragon jirgin kasa a tashan jirgin da ke Maiduguri a jihar. 

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne a yau Asabar 14 ga watan Oktoba inda su ka ce ‘yan sanda sun kama wadanda ake zargin mutum 6, Legit ta tattaro. 

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta yi nasarar cafke barayin ne bayan samun bayanan sirii daga mutanen gari. 

Punch ta kawo rahoton yadda ta samu labarin kamar haka: 

“An dakile shirin satar taragon jirgin kasa a Maiduguri bayan samun bayanan sirii daga wasu mutanen kirki. 

“Wadanda ake zargin tuni su ka shiga hannun jami’an sanda tare da tafiya da su don bincike.” 

Yayin da aka tuntubi kakakin Hukumar Jiragen Kasa, NRC, Mahmood Yakubu ya ce ba shi da masaniya kan faruwar lamarin inda ya ce a tuntubi manajan hukumar na yanki.

Post a Comment

0 Comments