Wata kotun shari'a da ke zama a Kwana Hudu a jihar Kano ta yi umurnin yi wa wani matashi dan shekaru 25, Yakubu Haruna, bulala 15 saboda satar rake.
Da farko, mai gabatar da kara, Aliyu Abidin Murtala, ya fada ma kotun cewa wani Abdullahi Muhammad, mazaunin Rimin Kebe, ya yi kai wa yan sanda a Zango kara cewa wanda ake karar ya sace masa sandar rake guda biyu.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa, wanda ake zargin ya amsa tuhumar da ake yi masa.
A kan haka ne Khadi na kotun, Nura Yusuf Ahmed, ya yi umurnin cewa a yi masa bulala 15 kasancewar wannan ne karo na farko da yake aikata laifin.
Comments
Post a Comment