“A Raba Aurenmu Da Mijina Saboda Mazakutarsa Ta Min Girma”.
Amarya Ta Gayawa Kotu Bayan Kwana Bakwai Da Aurensu Wata sabuwar Amarya ta nemi kotu ta raba Aurensu da Angonta bayan sati daya da yin bikinsu. Lamarin dai ya faru ne a wata kotu dake Samaru a Gusau jihar Zamfara, inda Amaryar mai suna Aisha ta bayyana wa kotu cewar, mijin ta yana yawan bukatar jima’i kuma mazakutarsa ta mata girma.
“A daren farko da mijina ya sadu da ni, maimakon na ji dadin abin, sai azaba na ji, saboda mazakutarsa babbace.”
“A rana ta biyu da muka sake saduwa lamarin ya kara kazanta, kuma anan ne na gano cewa ba zan iya jurewa ba.” Inji A’isha A karshe mijin Aisha ya amince da bukatar ta, inda ya ce ya yarda a raba auren nasu kamar yadda ta nema. -Idon Mikiya Picture not related to the story. #bloggingarewa
0 Comments