Ganin yadda rayuwa ta kara tsada a dalilin tashin kufin fetur, za ayi amfani da bashin ne domin a rabawa gidaje miliyan 15 a kasar.
Tinubu zai ba gidaje N25, 000 Masu karamin karfi ake sa ran za su amfana da N25, 000 kowace wata. Za a dauki watanni uku; Oktoba zuwa Disamba ana yin rabon..
Baya ga iyalan da za a rika rabawa dubunnan a duk karshen wata domin rage radadi, gwamnati za ta ba ma’aikata karin N35, 000 a wata.
Bashin Najeriya ya karu a 2023
Kafin nan Muhammadu Buhari ya yi nasarar karbo aron $800m daga babban bankin na Duniya domin a tallafawa mutum miliyan 50.
Rahoton da aka fitar ya nuna a cikin shekara guda, Najeriya ta tara bashin fiye da $1bn. Bayanan da aka samu daga Bankin duniya ya nuna daga Junairu zuwa Yuni, gwamnatin Najeriya ta karbi aron abin da ya kai $14.3bn.
A jeringiyar kasashen da su ka karbi aron bashin kudi a bana, Najeriya ce ta hudu a jerin.
Najeriya ta yi kamu a bankin duniya Ministan kudi watau Wale Edun ya zama shugaban kungiyar gwamnonin Afrika a bankin duniya, a makon nan aka samu wannan labari.
A shekaru 60 a tarihi sai yanzu ne kujerar nan ta iya isowa kan ‘dan Najeriya, kasar ta na da babbar dama a matsayin shugabar kungiyar.
0 Comments