Babu tabbacin shinkafa za tayi arha duk da bankin CBN ya halatta bada dala - Abis Fulani


CBN ya sanar da cire takunkumi wajen bada dala domin shigo da wasu kayayyaki 43 wanda a baya bankin ya cire hannu a kan su. 

Punch ta ce kungiyar OPS ta ‘yan kasuwa ta yabawa wannan mataki, ta na mai cewa hakan zai taimaka wajen samar da ayyukan yi a Najeriya. 

A wata sanarwa da bankin na CBN ya fitar a makon jiya, ya ce janye takunkumin zai rage adadin masu neman kudin kasar waje a kasuwar canji. 

Tsarin zai tabbatar da ‘yan kasuwa su ke juya farashin kudin ketare, kuma ana sa ran samun sauki wajen yadda farashi ya ke canzawa bini-bini. 
Wannan zai sa abinci ya rage tsada? 

A hirar da Legit Hausa ta yi da Dr. Usman Bello, ya shaida mana watakila CBN sun yi haka ne saboda ayi maganin masu yawan boye kayan abinci. Idan babban bankin zai bada kudi domin shigo da irinsu shinkafa daga kasashen waje, masana su na tunanin yawa zai jawo farashi ya karye. 

Dr. Usman Bello wanda masanin tattalin arziki ne a jami’ar ABU Zariya ya ce ba dole hakan ta faru ba, la’akari da farashin Dala-Naira a halin yanzu. 

"Ba zai yi tasiri ba idan sai an saye Dala da tsada, tun da babu rangwame, farashi ba zai canza ba, ‘yan kasuwa za su ji kyashin shigo da kaya." 

Post a Comment

0 Comments