Ƙasar Switzerland Ta Samar Da Na'urar Da Mutum Zai Iya Kashé Kansa
Wannan ita ce na'urar kashé kai da aka ƙera a ƙasar Switzerland, ta samu sahalewar fara aiki da ita a hukumance, a madadin mutum ya kashé kansa a gida da wuƙá, ko da igiya, ko ya fáɗo daga bene, yanzu waya kawai za ka buga a zo da ita har gida, a gaban 'yan uwa da abokan arziƙi ka mutu suna gani bayan an yi bankwana.
Kada a manta ƙasar Switzerland ita ce ƙasa mafi daɗin rayuwa ta zahiri a yanzu haka a Turai, ita ce kuma mafi yawan albashi, kyan yanayi, tsafta da kuma tsaro, duk da haka 'yan ƙasar sune kan gaba wajen kashé kansu a Duniya.
Tamabayar a nan ita ce, shin ko me ya sa?
0 Comments